Hukumar zaben Zimbabwe ta ayyana shugaba, Emmerson Mnangagwa, a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar da kashi 53 na ƙuri’un da aka kaƙa.
Mnangagwa ya doke babban abokin hamayyarsa Nelson Chimasa wanda ya samu kashi 44 na ƙuri’un.
Masu sanya idanu daga EU a zaɓen sun ce an yi amfani da rikici da razanarwa wajen tsoratar da masu zaɓe.
Babbar jam’iyyar adawa ta ki sanya hannu a kan takardar sakamakon zaben, sannan ta kaurace wa wajen da aka bayyana sakamakon zaben.
Tun da farko kafofin yada labaran ƙasar sun ruwaito cewa jam’iyyar Mista Mnangagwa ta samu nasarar lashe kashi biyu cikin uku na kujerun majalisar dokokin kasar.
Shugaban ƙasar zai fuskanci sabbin matsalolin da suka dabaibaye ƙasar ciki har da hauhawar farashi da rashin aikin yi da kuma cin hanci.


