fidelitybank

Miyar ganyen Lalo ta kashe mutane 12 a jihar Zamfara

Date:

Mutum 12 sun mutu a garin ‘Ɗaki Takwas da ke ƙaramar hukumar Anka ta Jihar Zamfara, bayan sun sha wata miyar ganyen lalo mai ɗauke da sinadarin maganin kashe ‘kwari.

Mutum 25 ne da suka fito daga gidaje biyu suka sha miyar a ranar Juma’a inda tun a lokacin suka fara rasuwa ɗaya bayan ɗaya.

Yanzu haka dai akwai mutum tara daga cikinsu da ke karɓar kulawa a asibiti.

Dakta Yusuf Abubakar Haske, shi ne Daraktan Kula da Lafiyar Al’umma kuma jami’i mai Kula da cututtuka masu yaɗuwa a jihar, ya bayyana yadda al’amarin ya faru cikin tattaunawar da ya yi da BBC.

Jami’in ya tabbatar da cewa shan miyar da aka yi da ganyen lalon ce ta yi sanadiyar mutuwar mutanen.

“Manomi ne ya je ya yi feshin kwari da wasu hakukuwa da ba ya so, daga cikin hakukuwan akwai wani ganye da ake kira lalo, wanda ana miya da shi a gidajenmu na Hausa. Su kuma mutanen ba su san ya yi ba.”

“Ya yi feshin da safe, su kuma suka je da rana domin nemo ganyen da za su yi miya. Daga bisani sai suka kamu da amai da gudawa da zubar da yawu. Daga nan ne aka ɗauke su zuwa asibiti, inda ma’aikatan lafiya suka zo domin ba su taimakon gaggawa.

Jami’in lafiyan ya ce kasancewar wasu sun fi wasu shan miyar, sai ya kasance wasu sun mutu a gida yayin da wasu kuma a wani asibiti a Anka suka mutu, wasu kuma sai da aka kai su Babban Asibitin Tarayyar jihar suka mutu.

Sai dai jami’in ya ce Jihar Zamfara a shirye ta ke domin fuskantar ko-ta-kwana kan wannan lamari.

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp