Ministan shari’a kuma babban lauyan tarayya (AGF), Abubakar Malami ya shiga takarar neman kujerar gwamnan jihar Kebbi a 2023.
Ministan ya bayyana aniyar sa ne a ranar Alhamis, kuma zai nemi tikitin a jam’iyyar APC kamar yadda Naija News ta rawaito.
A cewar Malami, ya shiga takarar ne domin amsa kiraye-kirayen da jama’ar sa suka yi na yi wa jihar hidima a matsayin Gwamna