fidelitybank

Ministan shari’a Abubakar Malami na neman takarar kujerar Gwamna a 2023

Date:

Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar gwamna a jihar sa a shekarar 2023.

Malami wanda ya bayyana a gaban magoya bayan sa a jihar Kebbi ya yi alkawarin ba zai ci amana su ba.

“Idan Allah cikin rahamarSa, kuma komai ya tafi daidai, ni a matsayina na dan siyasa zan tsaya takarar Gwamnan Jihar Kebbi. Ina neman goyon bayan ku.

“Ina so in sanar da cewa lallai zan tsaya takara, kuma a don haka ina dogara ga addu’o’in ku da goyon bayan ku, domin mu yi aiki tare da tsira tare. Ba ni da tarihin cin amana kuma ba zan ci amanar ku mutane ba. Zan yi muku aiki,” ya shaida wa magoya bayansa a harshen Hausa, a wani faifan bidiyo da aka gani a ranar Litinin.

A cewar jaridar Thisday, Babban Lauyan Najeriya, ya yi nuni da cewa shugabanni na bukatar mabiya kuma mabiya su kuma suna bukatar shugabanninsu domin ganin ‘yan kasa sun amfana, kamar yadda ya yi alkawarin yin aiki ba dare ba rana domin juya rayuwar ‘yan kasa.

A baya dai Malami ya shaidawa abokansa na kusa aniyarsa ta tsayawa takarar zaben jihar Kebbi.

naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp