A daren jiya Alhamis ne rahotanni suka nuna cewa ministan harkokin wajen Iran ya isa babban birnin Beirut na Lebanon.
Kafofin yaɗa labarai na ƙasar Lebanon ne suka ruwaito hakan.
“Jirgin saman Iran ya sauka a filin jirgin Rafic Hariri Internation tare da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi,” kamar yadda kafar dillancin labarai na NNA ta ruwaito.
Wannan ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila take ƙara zafafa hare-hare a birnin Beirut, ciki har da wani filin jirgin ƙasar.


