Ministan harkokin jin kai, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa.
An tabbatar da nadin Yilatda a ranar Alhamis, yayin taron kwamitin zartarwa na kasa, NEC, taron jam’iyyar APC.
Zai maye gurbin Abdullahi Ganduje, wanda ya yi murabus a watan da ya gabata, saboda matsalolin lafiya.
Mataimakin shugaban na kasa (Arewa), Ali Bukar Dalori, ya fara aiki a matsayin mukaddashin bayan Ganduje ya sauka.
Masu ruwa da tsaki sun yi tsammanin hukumar zabe za ta amince da aikin Dalori tare da ba shi lokacin da zai shirya babban taron kasa na zaben shugaban kasa.