Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Marlin Sylva ya yi nasara a karar da Mawallafin Point Blank News, Mista Jackson Ude, a wata Kotun Lardi ta Gabashin Pennsylvania ta Amurka.
An tattaro cewa, Jackson Ude ya yi a cikin wata jarida ta yi zargin cewa ministar na da hannu wajen karkatar da kudade.
Daga cikin wasu wallafe-wallafen da ake zargin suna da nufin bata sunan Ministan, Ude ya zargi Timipre da bayar da cin hancin dalar Amurka dubu goma ga kowane dan majalisar dokokin kasar a wani yunkuri na yin tasiri ga ‘yan majalisar su amince da kudirin dokar masana’antar man fetur (PIB).


