Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya gargaɗin ‘yan siyasa da su riƙa martaba tsanin da ya taimaka musu wajen kai wa matsayin da suke.
Rahotonni sun ambato mista Wike – wanda a baya-bayan nan ya samu saɓani da wanda ya gaje shi a masatyin gwamnan jihar, Siminalayi Fubara – na bayyana haka a lokacin da tawagar wasu sarakunan gargajiyar jihar suka ziyarce shi a gidansa dake birnin Fatakwal.
Ministan na Abuja ya ce ya ce ”Kada ka yarda ka karya tsanin da ya taimaka maka wajen hawa inda kake, domin idan ka tashi sauko dole za ka buƙace shi, alhalin kuma baya nan”.
”Ka bar tsanin a wurin domin wasu ma za su samu su hau”, in ji shi.
Sarakunan gargajiyar waɗanda suka ziyarci tsohon gwamnan a daidai bikin zagoyawar ranar haihuwarsa, sun ce zaman lafiyar jihar shi ne babban muradinsu.
Mista Wike ya kuma tabbatar wa da sarakunan cewar shi ma a nasa ɓangare yana maraba da zaman lafiyar jihar.
A baya-bayan ne dai Mista Wike ya samu matsala da gwamnan jihar, lamarin da ya sa a cikin makon da ya gabata wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar 27 suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, wani mataki da ya sa majalisar mai ragowar mambobi biyar ta ce ta kori ‘yan majalisar 27.
Daga baya kuma gwamnan jihar ya bayar da umarnin rusa ginin majalisar, inda ya ce an yi hakan ne saboda rashin ingancin ginin.