fidelitybank

Mika wa Atiku tikitin takarar shugabancin kasa zai haifar da wargajewar Najeriya – Ƙungiyar Inyamurai

Date:

Kungiyar matasan Ohanaeze ta Inyamurai (OYC) ta gargadi jam’iyyar PDP kan zaben tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023.

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamrade Igboayaka O. Igboayaka, ya yi wannan gargadin a lokacin da yake magana a Owerri, babban birnin jihar Imo.

A cewar sa, PDP ta mika wa tsohon mataimakin shugaban kasa tikitin takarar shugabancin kasa a 2023 zai haifar da wargajewar Najeriya gaba daya.

Shugaban matasan Ohanaeze, ya kuma lura da cewa majalisar ta fusata ne kan, lokacin da Atiku Abubakar ya yi na karbar tikitin takarar shugaban kasa na PDP.

Ya ce; “Idan PDP ta ki amincewa da tikitin takarar shugaban kasa na yankin Kudu maso Gabas, abin da kawai matasan Igbo sama da miliyan 50 ya kamata su tabbatar shi ne, su ci gaba da rike Najeriya daya ta hanyar zabar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC daga yankin Kudu maso Gabas, kuma babu wani ofishi/tuta na PDP daga matakin unguwanni har zuwa jiha da za a kafa a yankin Kudu maso Gabas. Za mu yi yaki da PDP kamar yadda Yakubu Gowon ya yi domin a mayar da Najeriya kasa daya.”

A cewar majalisar, “Ya kamata Atiku Abubakar ya bi tarihin kafa PDP daga G34 karkashin jagorancin Dr. Alex Ekwueme kafin ta zama jam’iyyar siyasa, domin tabbatar da cewa, yankin Kudu maso Gabas ya fi kowace shiyya a Najeriya.”

www.nigeriannewspapers.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...
X whatsapp