Gimbiya Rukaiya Atiku Abubakar, matar tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ta bayyana cewa mijin ta ne kadai ke da goyon bayan mata.
A cewarta, saboda haka ne tsohon mataimakin shugaban kasar ya ware dala biliyan 10 domin karfafawa mata da matasa idan har aka zabe shi kan karagar mulki.
Rukaiya tare da sauran mambobin kungiyarta PRACO, sun je jihar Bauchi ne a ranar Talatar da ta gabata domin gudanar da gangamin goyon bayan matan Arewa maso Gabas ga mijinta, Atiku Abubakar.
“Mijina, Atiku Abubakar, shi ne dan takarar shugaban kasa daya tilo a zaben 2023 mai gabatowa wanda ke goyon bayan shigar mata da matasa a harkokin mulki.
“A kan haka ne ya yi alkawarin ware dala biliyan 10 don karfafa matasa da mata,” in ji ta.
Rukaiya, daya daga cikin matan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a 2023, ta taka rawa sosai a yakin neman zaben Atiku na zabe mai zuwa.
Ta yi alkawarin cewa idan Atiku ya zama shugaban kasa, zai yi aiki don samar da mafita ga dimbin matsalolin da suka shafi ci gaban mata.