Lionel Messi ya ci kwallo ta 800 a karawar da Argentina ta doke Panamavda ci 2-0, a wasan farko tun bayan da ta lashe kofin duniya a Qatar na 2022.
Mai shekara 35 shine ya ci na biyun a bugun tazara, ya zama na biyu bayan Cristiano Ronaldo, wanda ke kan gaba a wannan bajintar ci kwallaye da yawa.
Messi ya ci kwallo 672 a kaka 17 da ya yi a Barcelona da 29 da ya zura a raga a Paris St Germain.
Haka kuma ya ci wa Argentina kwallo 99 har da biyun da ya ci Faransa a wasan karshe a kofin duniya a Qatar.
Messi ya ci Panama na biyu a bugun tazara a minti na 89 a karawar da suka yi a filin wasa na Monumental de Nunez Stadium a Buenos Aires.
Thiago Almada ne ya fara cin kwallo a minti na 11 da fara wasan.