Lionel Messi ya zama dan wasa na uku da ya wuce kwallaye 100 a duniya.
Dan wasan mai shekaru 35 ya ci hat-trick a wasan da Argentina ta doke Curacao da ci 7-0 a wasan sada zumunci a ranar Talata.
Kwallaye uku da Messi ya ci ya kai 102.
Shahararren dan wasan na Paris Saint-Germain Messi, ya ci kwallaye 100 a wasa na 174 da ya buga wa kasarsa, bayan da ya ci kwallo ta 99 a duniya kuma ta 800 a rayuwarsa a wasan da suka doke Panama da ci 2-0 a ranar Alhamis din da ta gabata.
Messi, ya ci gaba da zama na uku a jerin wadanda suka fi kowa zura kwallaye a duniya, bayan Cristiano Ronaldo na Portugal, wanda yanzu yake da 120 da Ali Daei na Iran, wanda ya ci 109 kafin ya yi ritaya a 2007.