Ɗan kwallon kafar Argentina da Inter Miami Lionel Messi ya lashe kyautar fitaccen ɗan kwallon kafar Fifa na bana.
Messi ya samu kyautar ne bayan buge abokan karawarsa Erling Haaland da kuma Kylian Mbappe.
A bangaren masu horaswa, Pep Guardiola ya zama gwarzon mai horaswa na shekara, yayin da ‘yar kasar Jamus mai horas da Ingila ta mata ta lashe kyautar ta bana.


