Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain, Lionel Messi, ya sauka a birnin Barcelona yayin da jita-jitar komawar sa Camp Nou ke kara kamari.
A cewar babban dan jarida Gerard Romero fitaccen dan wasan na Argentina ya sauka a birnin na Kataloniya, wanda ya kara dagula jita-jita.
Shahararren dan jaridar ya kara da cewa wannan ba ziyarar ta yau ba ce ga gwarzon dan wasan da ya lashe kofin duniya, kamar yadda BarcaWorldwide ta wallafa a shafin Twitter.
Ya bayyana cewa Messi yana Barca tare da iyalansa da kuma kaya masu yawa.
“Wannan ba ziyarar ta yau da kullun ba ce ga Messi a Barcelona kamar yadda Pepe Costa (na hannun dama na Messi) ke ɗauke da akwatuna 15. Dangane da ziyarar da ya kai a baya, Leo Messi ya fita ta wata kofa ta daban a filin tashi da saukar jiragen sama a wannan karon domin kada kowa ya gani a Barcelona.
“Lionel Messi ya fi kusa da komawa Barcelona. Dole ne mu sanya ido a cikin kwanaki masu zuwa saboda akwai motsi da ka iya faruwa.”
Kwantiragin Messi a Princes des Parc za ta kare ne a karshen kakar wasa ta bana, kuma tattaunawa kan sabunta ta na neman yin tsami, inda Barcelona ke son dawo da tarihinta kyauta.


