Dan wasan gaban Argentina, mai shekara 36, ya bayar da ƙwallo aka ci har sau biyu a wasan da Inter Miami ta kara da FC Cincinnati a gasar US Open, wanda aka tashi 3-3 bayan ƙarin lokaci.
Wannan dai shi ne karon farko da Messi ya kasa zura kwallo a raga tun da ya koma Inter Miami.
Amma ya samu nasarar zura ƙwallo a bugun fenareti , inda suka tashi da ci 5 – 4 a wasan da aka buga a filin wasa na Ohio.
A ranar Asabar Inter Miami ta lashe kofinta na farko bayan doke Nashville a wasan ƙarshe na kofin League.
Wannan shi ne babban kofin na farko da kungiyar ta samu tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2020.
A yanzu kungiyar za ta buga wasan ƙarshe a gasar cin kofin US Open karon farko, gasar kwallon kafa mafi daɗewa kuma mafi shahara a Amurka, wadda aka fara tun shekarar 1913.
Miami ba ta yi rashin nasara ba a wasanni takwas bayan da ta sayi Messi da takwarorinsa na Barcelona Sergio Busquets da Jordi Alba.


