Tauraron ɗan wasan Argentina, Lionel Messi, ya kafa tarihin cin ƙwallo a kowane mataki na Gasar Kofin Duniya.
Shi ne ɗan ƙwallo na farko da ya jefa ƙwallo a raga a matakin rukuni, da na kwaf ɗaya, da na ‘yan 16, da na kusa da na ƙarshe, da na kusa da ƙarshe, da kuma ƙarshe.
Yanzu haka Argentina na ci gaba da cin Faransa 2-0 a wasan da ke gudana a filin wasa na Lusail da ke Qatar.