Dan jaridar kwallon kafar Faransa, Daniel Riolo, ya soki dan wasan gaban Paris Saint-Germain Lionel Messi da tafiya zuwa Saudi Arabiya, kwana guda bayan kungiyarsa ta sha kashi a hannun Lorient da ci 3-1 a gasar Ligue 1.
A ranar Litinin ne Messi ya tafi kasar Saudiyya domin gudanar da aikinsa a matsayin jakadan kasar.
Sai dai abin da Messi ya yi ya sa Riolo ya fusata.
Riolo ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa “Ranar da kungiyar ka ta sha kashi, kai ka tafi Saudiyya don tallata kanka.”
Messi bai taka rawar gani sosai ba yayin fafatawar da suka yi da Lorient, saboda bai yi rajistar bugun daga kai sai mai tsaron gida ba a ranar Lahadi.