Shugaban Paris Saint-Germain, Nasser Al-Khelaifi ya zargi Lionel Messi da rashin “girmama” kulob din Ligue 1 bayan tafiyarsa a watan Yuni 2023.
Messi ya amince a watan Satumban da ya gabata cewa ya ji haushin yadda PSG ba ta karrama shi ba bayan bajintar da ya yi a gasar cin kofin duniya a 2022.
“Ba mugun mutum ba ne amma ba na son shi.
“Zan ce, ba don shi kaɗai ba amma ga kowa da kowa, muna magana lokacin da muke wurin, ba lokacin da muka tafi ba. Wannan ba salon mu bane…
“Ina matukar girmama shi [Messi] amma idan wani yana son yin magana mara kyau game da Paris Saint-Germain daga baya, hakan ba shi da kyau. Wannan ba girmamawa ba ne, ”Al-Khelaifi ya fada wa RMC Sport.
Messi ya zura kwallaye biyu a wasan karshe da Faransa a Qatar.
Ya kuma rama fanareti a bugun daga kai sai mai tsaron gida inda Argentina ta ci 4-2 a bugun fenariti.