fidelitybank

Mele Kyari na tsaka mai wuya a kan matatar Dangote

Date:

Majalisar Wakilai ta ce za ta yi kira da a kori babban jami’in kamfanin mai na Najeriya National Petroleum Company Limited, NNPC, Mele Kyari, idan har abin da suka bayyana a matsayin “yunkurin lalata matatar dangote” bai tsaya nan take ba.

Mataimakin kakakin majalisar, Philip Agbese ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Asabar.

Agbese ya bayyana cewa tuni ‘yan majalisar suka bukaci a kori shugabannin hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya NMDPRA.

Ya lura cewa duka hukumomin biyu – NNPCPL da NMDPRA – sun nuna cewa suna da sha’awar lalata matatar Dangote.

Ya bayyana cewa ‘yan Najeriya da dama sun janye zanga-zangar wahala da ake shirin yi, sai dai ya kara da cewa suna son ganin an kori Kyari idan hakan zai tabbatar da tafiyar da kasar cikin sauki.

A cewarsa, majalisar za ta binciki rikicin da ke faruwa tsakanin matatar Dangote da hukumar NMDPRA.

Agbese ya ce binciken ya yi daidai da kudurin majalisar na kare dukkan kadarorin kasa da muhimman ababen more rayuwa na tattalin arziki, kamar matatar Dangote.

Ya ce: “Mun dade muna gani ta hanyar yin kamfen don bata sunan matatar man Dangote da kuma la’akari da mummunan tasirin da hakan ya haifar da firgici a kasar.

“A rubuce ne cewa majalisar ta umarci shugaban kasa ya kori shugaban NMDPRA.

“Majalisar wakilai ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin kira da a kori Mele Kyari, idan har yunkurin lalata matatar man, wani kadarorin kasa, bai tsaya nan take ba.”

Idan ba a manta ba tun da farko kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ya jagoranci tawagar majalisar zuwa kamfanin matatar man dangote da ke Legas.

Abbas ya ce ziyarar ta ba da bayanai masu ma’ana da za su jagoranci matakan majalisar da kuma yanke shawara.

Ya ce majalisar na kokarin samar da yanayi mai dacewa da kasuwanci don sanya Najeriya ta zama makoma ga masu zuba jari na ciki da waje.

sani ahmad

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp