Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya amince da gagarumin rinjaye wani ƙudiri da ke neman tsagaita wuta nan take bisa muradan ayyukan jin-ƙai a Zirin Gaza.
Ƙudirin wanda kasar Jordan ta gabatar a madadin rukunin kasashen Larabawa a yammacin jiya Juma’a ya kuma yi Alla-wadai da dukkan wasu ayyukan tarzoma a kan fararen hula na Falasdinawa da Isra’ila, ciki har da dukkan “hare-haren ta’addanci da kuma na ba-ji-ba-gani”.
Ƙudirin ya yi kira a bai wa fararen hula kariya sannan a shigar da kayan agaji Gaza ba tare da iyaka ba.
Ƙasashe 120 ne suka kaɗa ƙuri’ar amincewa, 14 suka ƙi nuna goyon baya, yayin da 45 suka ƙaurace wa jefa ƙuri’ar.
Ba lallai ne a yi aiki da ƙudirorin Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ba, amma suna ɗauke da alhakin sanin ya kamata ga ɗaukacin mambobin MDD.