Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dakarunta na wanzar da zaman lafiya da ke a kudancin Lebanon ba za su je ko ina ba, inda ta sake yin fatali da kiran da Isra’ila ta yi na janye su.
Dakarun MDD da dama ne suka jikkata a harin da sojojin Isra’ila suka kai wa Hezbollah.
Mataimakin babban sakataren MDD, Jean-Pierre Lacroix, ya jaddada cewa dole ne a tabbatar da tsaron dakarun.
Ya ce babban kiran da su ke yi ga dukkan ɓangarorin shi ne su mutunta hakkin da ya rataya a wuyansu na kare lafiya da tsaron dakarun wanzar da zaman lafiyar.