Majalisar Dinkin Duniya ta sake jaddada kiranta na neman tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza.
Wata Sanarwar a madadin shugabannin hukumomin Majalisar Dinkin Duniya goma sha daya, tare da ƙungiyoyin agaji guda shida, ta bukaci Isra’ila da ta kare fararen hula tare da ba da damar shigar da ƙarin abinci da ruwa da magunguna da kuma mai zuwa Gaza.
Ta ce an yi wa jama’ar Gaza kawanya tare da hana su samun abubuwan da ake bukata na rayuwa.
Ta ce salwantar rayukan ma’aikata 88 na hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinnawa ta Majalisar Dinkin Duniya shi ne mafi girman mace-macen da Majalisar Dinkin Duniya ta fuskanta a yaki daya.