fidelitybank

MDD: Gwamnatin Borno ta haramta jin kai a jihar

Date:

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya haramta wa kungiyoyi masu aikin jin-kai bayar da agajin abinci ko wasu kayayyaki ga ’yan gudun hijirar a jihar.

Gwamna Babagana Zulum ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aike wa kungiyoyin ta hannun Ofishin kula da ayyukan jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya.

Wasikar ta bukaci masu aikin agajin da su mayar da hankali wajen bunkasa harkokin dogaro da kai tare da rufe bayar da tallafin kayan abinci.

Gwamnati ta kuduri aniyar rufe dukkan sansanonin ’yan gudun hijira da aka kafa a hukumance a Maiduguri a watan Disamba.

Gwamnan ya kara da cewa shirin rufe sansanonin ’yan gudun hijirar ya kunshi taimaka wa jama’a su tsaya da kafafunsu.

Zuwa yanzu dai Gwamnatin Jihar ta Borno ta rufe sansanonin ‘yan gudun hijira guda hudu a Maiduguri, ta kuma sake tsugunar da mutanen da ke wuraren a garuruwansu na asali. A cewar Aminiya.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...

Mu na gargadin Isra’ila kan korar al’ummar Gaza daga yankin su – MDD

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya...

Rikici ya kuma balle a Syria

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan'adam sun ce, wani sabon rikici...

Tsofaffin ‘Yansanda na da ‘yancin yin zanga-zanga – A Cewar Amnesty

Ƙungiyar Amnesty International ta ce tsofaffin ƴansandan Najeriya girmamawa...

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...
X whatsapp