fidelitybank

MDD da ECOWAS ta gargadi Najeriya a kan zaben 2023

Date:

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Bunƙsa Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, sun gargaɗi Najeriya kan batun haddasa rikici a zaɓen 2023.

Sun bayyana hakane a wani taron tattaunawa da kungiyar shiga tsakani na jam’iyyu da masu ruwa da tsaki da suka fito daga yankin arewa ta tsakiya da arewa maso gabas kan kaucewa tada fitina a Jos, babban birnin jihar Filato a ranar Talata.

MDD ta ce muddin ba a ɗauki mataki ba, za a iya samun rashin zaman lafiya a faɗin yankin.

Ita ma ECOWAS ta ce idan rikici ya ɓarke a Najeriya, babu wata ƙasa a yankin sahara da za ta iya bai wa ‘yan gudun hijirar ƙasar mafaka saboda yawansu.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa sama da mutane 30 ne aka ruwaito mutuwarsu yayin da da yawa suka jikkata a rikice-rikice gabanin zaɓen 2023 a sassan daban-daban na Najeriya.

An kuma kai wa ofisoshin hukumar zaɓe mai zaman kanta hare-hare a wasu sassa na Najeriya musamman ma kudu maso gabas, inda ake zargin kungiyar ‘yan awaren Biafra da kai hare-haren wanda ya yi sanadiyyar rasuwar jami’an INEC da kuma jami’an tsaro da dama.

nan news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp