Mahaifiyar fitaccen dan wasan kwallon kafa Kylian Mbappe na Faransa ta karyata wani rahoto da ke cewa dan nata ya amince ya tsawaita zamansa a kungiyar Paris St. Germain da karin wasu shekaru uku, kuma ya fasa komawa kungiyar Real Madrid.
Talabijin din Channels ta rawaito cewa, Jaridar Le Parisien na cewa, masu kungiyar PSG – wato attajirai ‘yan kasar Qatar – sun yi wa Mbappe tayin albashin euro miliyan 50 a kowace kakar wasa da kuma wani alawus na euro miliyan 100 idan ya amince ya yi zamansa a kungiyar.
Sai dai mahaifiyar Mbappe, Fayza Lamari ta wallafa wani sakon Tiwita, wanda a ciki ta ce ba a kulla wata yarjejniya ba da dan nata:
“Ba a kulla yarjejeniya ba da Paris St. Germain (kuma ba a kulla ta da wata kungiyar ba)”, ta kuma ce “ana can ana tattaunawa kan makomar Kylian, saboda haka nake rokon ku da ku ba shi damar yanke hukuncin da ya dace da shi.”
Kylian ya dade yana bayyana sha’awarsa ta komawa kungiyar Real Madrid nan gaba, kungiyar da a wannan makon ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai, kwanaki kadan bayan ta lashe gasar lig ta Sfaniya na 35 a tarihinta.