Mutanen yankin Ɗan Kurmi cikin ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara sun ce, sun ƙara shiga tashin hankali, bayan wani harin ‘yan fashin daji a jiya Lahadi.
Bayanai sun ce, ‘yan fashin dajin a kan babura sun kashe mutane ciki har da wani gwarzon ɗan sa-kai a ƙauyen Gidan Adi, tare da sace dabbobi har ma da ƙone-ƙone.
Lamarin na zuwa ne daidai lokacin da a jihar Filato da ke arewa ta tsakiya, rahotanni ke cewa ‘yan sa-kai sun tarwatsa wata dabar ‘yan fashin daji a ƙaramar hukumar Wase. In ji BBC.


