fidelitybank

Mazauna Maiduguri na murnar dawowar wutar lantarki bayan shafe wata 11

Date:

Wasu daga cikin al’umma a Maiduguri babban birnin jihar Borno, sun tashi da murnar, bayan dawowar wutar lantarki da a ka yi musu a yankunan su.

Tun cikin watanni 11 bayan katsewar wutar lantarki, lamarin da ya biyo bayan lalata kayayyakin aiki da manyan layukan wutar lantarki a birnin da ‘yan Boko Haram su ka yi.

Lamarin dai ya gurgunta masu kananan sana’o’i tare da tilastawa mutane yin amfani da injin janareta a matsayin madadinsu.

An fara dawo da wutar lantarki a yankin Bulunkutu a ranar 22 ga watan Disamba sannan kuma a unguwar Pompamari dake cikin birnin.

Mazauna yankin musamman matasa masu kananan sana’o’i kamar cajin waya da bushewar da sana’o’i musamman a kasuwar waya ta Jagwal da kuma mata masu sayar da kayan sanyi da bulo na kankara da masu rijiyoyin burtsatse da kananan yara na daga cikin mutanen, wanda su ka nuna murna da dawowar wutar lantarki.

Gwamnatin jihar Borno ta shiga tsakani tare da goyon bayan shirin dawo da wutar lantarki a Maiduguri, musamman a kokarin da a ke na sake hada sabbin gine-gine da layukan wutar lantarki daga Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Rahotanni na cewa maharan na ci gaba da lalata wasu wuraren kamar igiyoyi, lamarin da ya kawo jinkirin dawo da cikakken wutar lantarki a tsakiyar birnin.

Wani mazaunin Bulunkutu Kasuwa, Ibrahim Ali, ya shaida wa wakilinmu cewa, dawo da wutar lantarkin ya haifar da farin ciki a Bulunkutu a tsakanin masu sana’a da ‘yan kasuwa da masu injinan nika.

Ya ce, “Mun samu kiran waya da dama, domin tabbatar da ganin an dawo da hasken. Na tuna cewa wasu abokaina sun kira waya domin tabbatar da ko gaskiya ne cewa an dawo da haske. Ya zo kamar bakon labara, amma muna matukar godiya da dawowar haske a yankinmu. Mun yi imanin cewa da yawa za su koma ƙananan sana’o’insu kuma rayuwa za ta sami kwanciyar hankali sosai”. In ji Ibrahim.

Wani ma’aikacin kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Yola (YEDC) da bai so a bayyana sunansa ba, ya bayyana cewa, yawancin taransfoma da ke cikin birnin sun cire wayoyin wutar da DisCo su ka saka, domin adanawa.

punch news paper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp