fidelitybank

Mazauna Kudu ku gaggauta bayyana masu yin kisa – Buhari

Date:

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya nemi shugabanni da mazauna yankin kudu maso gabashin ƙasar da su bayyana waɗanda ke kashe baƙi da jami’an tsaro a yankin “idan sun san inda suke”.

Kiran shugaban na zuwa ne kwana ɗaya bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda huɗu ranar Asabar da kuma kisan fararen hula shida a farkon mako a Jihar Imo.

Rundunar ‘yan sandan ƙasar ta ce mayaƙan ƙungiyar IPOB ne suka kai harin kan jami’anta a ofishinsu da ke Agwa na Jihar ta Imo.

Buhari ya kira kisan a matsayin “na ta’addanci” sannan ya nemi shugabannin yankin da “su dinga nuna ƙyamar kashe-kashen a fili don tsare al’adu da addinin mutane”.

“Waɗanda suka san mutanen da suka aikata hakan su bayyana su,” in ji shi cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa Garba Shehu ya fitar ranar Asabar.

Shugaban ya kuma yi alƙwarin gudanar da bincike “na gaggawa” don gano “waɗanda suka aikata ta’addanci”.

daily post today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp