Sanata Sani Musa, mai wakiltar gabashin jihar Niger inda ‘yan bindiga suke cin karen su babu babbaka, ya yi kira ga mazauna kauyuka da matasa da su hada kawuna don ganin an zakulo gami da wartakar ‘yan bindiga a jihar Neja.
Sanatan ya bukaci gwamnatin tarayya ta samar da tabbataccen sansanin sojoji a yankunan da ake yawan kai hare-hare a jihar.
Vanguard ta rawaito cewa, an samu labarin yadda wasu mazauna kauyuka suka zama ‘yan leken asiri ga yan bindiga, wanda hakan ke share wa yan ta’adda hanyar kai farmaki a yankunan.
Ya yi kira ga jami’an tsaron da su yi amfani da dabarbarun zamani wajen ganin sun yi gaba da gaba da ‘yan ta’addan kamar yadda ya roki gwamnatin tarayya da ta samar da tabbataccen sansanin sojoji a yankunan da ake yawan kai hari.