Al’ummar jihar Kano, musamman magoya bayan manyan jam’iyyun siyasa biyu na jihar APC da NNPP, sun wayi gari cike da zaƙuwa gabanin sanar da wani hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, nan da ‘yan sa’o’i cikin Juma’ar nan.
Hukuncin kotun, wadda ke zamanta a Abuja, yana da matuƙar muhimmanci ga siyasar jihar, mafi yawan jama’a da harkokin kasuwanci a arewacin Najeriya, kuma ginshiki ne ga makomar siyasar Gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna, aƙalla tsawon shekara huɗu nan gaba.
Abba Kabir Yusuf ya garzaya gaban kotun ɗaukaka ƙara ne, bayan kotun ƙorafin zaɓe ta jihar Kano a ranar 20 ga watan Satumba, ta rushe nasarar da ya samu, inda ta ce abokin takararsa na jam’iyyar APC Nasir Yusuf Gawuna ne halastaccen wanda ya ci zaɓe.
Kotun ta soke sama da 165,000 a cikin ƙuri’un Abba Kabir Yusuf na NNPP, bisa hujjar cewa ba su inganta ba, saboda rashin sa hannu da kwanan wata da kuma hatimin hukumar zaɓe.
Jam’iyyar APC ta roƙi kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar Gwamna Abba Kabir.
Takara tsakanin ɓangarorin biyu, na ɗaya daga cikin mafi zafi da aka gani kafin zaɓen 18 ga watan Maris a Najeriya, kuma ga alama har yanzu, yanayin siyasar bai daina tafarfasa ba, wata takwas bayan kammala zaɓe.
Hukumomin tsaro a Kano, tun farkon wannan mako sun ce sun tura ƙarin jami’ai da kayan aiki zuwa manyan fuskokin garin, don hana faruwar tashin hankali, da kuma kare rayuka da dukiyar al’umma, tun kafin sanar da hukuncin.
Dukkan ‘yan takarar a zaɓen da ya wuce, suna da alaƙa da jiga-jigan ‘yan siyasar Kano biyu, Rabi’u Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje, tsoffin gwamnonin jihar da ke kan ganiyarsu har yanzu, sannan tsoffin manyan aminan juna, kafin su ɓaɓe a tafiyar siyasa.
Rundunar ‘yan sandan Kano dai ƙarƙashin kwamishinanta, Mohammed Usaini Gumel, ta gudanar da taron gaggawa da shugabannin jam’iyyun APC da NNPP a jajiberen wannan rana ta yanke hukunci.
Ta ce sun ɗauki matakai da haɗin gwiwar sojoji da sauran hukumomin tsaro a jihar don ganin ba a fuskanci rashin zaman lafiya a yayin, da kuma har bayan hukuncin kotun ba.
Kwamishina Mohammed Usaini ya kuma ce, sun tattauna, kuma sun samu tabbaci daga shugabannin jam’iyyun biyu cewa za su yi duk abin da ya wajaba don ganin ba a kawo hargitsi, saboda hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ba a Kano.