Har yanzu mazauna cikin ƙwaryar birni da kewaye a jihar Kano, na cigaba da nuna murna, sakamakon samun labarin matashin nan mai laƙabin Burakita ɗan unguwar Ɗorayi dake ƙaramar hukumar Gwale, da samun labarin rasuwarsa.
Matashin an daɗe ana ƙalubalantarsa da salwantar da rayukan al’umma da muggan makamai da aikata ƙwacen kadarorin al’umma.
Haka kuma an daɗe ana tuhumar sa da haɗa guggun matasa suna aikata kisan kai a jihar.
A yammacin juya Litinin ne dai rundunar ‘Yansandan Kano ta bakin kakakin ta, ASP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbata da mutuwar Burakita ga manema labarai, cewa matashin suna tuhumar sa da laifin aikata fashi da makami tare da kashe al’umma.
Ya kuma ce, bayan sun yi artabu da wasu mutane da ake zargi suna fakonsa, inda suka raunata shi, bayan an kai shi asibiti ya mutu.
Tuni dai mutane da dama suka bayyana farin cikin su na samun labarin mutuwar Burakita, wanda suka bayyana cewa, dama ya daɗe yana addabar al’umma kuma an kasa ɗaukar mataki a kansa.


