Mazauna garin Goningora da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, sun tare hanyar Abuja zuwa Kaduna, sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa al’ummarsu.
‘Yan ta’addan masu zubar da jini sun kai wa al’umma hari a daren ranar Laraba, inda suka kashe akalla mutane biyu, yayin da wasu bakwai suka yi garkuwa da su.
A fusace da faruwar lamarin, mazauna garin sun fito kan tituna a safiyar ranar Alhamis, inda suka tare babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Wannan ci gaban ya haifar da cunkoson ababen hawa a kan titin, lamarin da ya sa masu ababen hawa da matafiya da dama suka makale.
Harin na baya-bayan nan da aka kai kan al’ummar Goningora ya zo ne kwanaki bakwai bayan da sojoji suka kashe wani fitaccen sarkin ‘yan bindiga, Boderi Isyaku da wasu mayakansa a karamar hukumar Chikun.