fidelitybank

Maza 2 sun shiga hannun hukuma da zargin garkuwa da kisa a Bauchi

Date:

Jami’an hukumar tsaro ta Civil Defence a Jihar Bauchi, sun kama wasu maza biyu bisa zargin yin garkuwa da kashe wata yarinya ‘yar shekara biyar bayan karbar kudin fansa a hannun iyayenta.

Yayin gabatar da wadanda ake zargin gaban manema labarai a hedikwatar NSCDC da ke Bauchi a ranar Litinin, kwamandan jihar, Nuruddeen Abdullahi, ya ce mutanen sun yi garkuwa da yarinyar ne a kofar gidansu, inda suka tafi da ita karkashin wata gada suka shake ta suka saka ta cikin buhu duk da cewa sun karbi kudin fansa a wajen iyayenta.

Rahotanni sun ce daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da yarinyar makwabcinsu ne.

Yarinyar mai suna Khadija, makwabcin nasu ya sace tane a lokacin da take wasa a kofar gida, inda da farko ya nemi a bashi kudin fansa naira miliyan daya, amma daga bisani aka tsaya a kan naira dubu 150.

Lamarin dai ya faru ne a garin Na Rabi, da ke Bauchi.

sani ahmad

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp