Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa tunanin mayar da ‘yan daba 50 zuwa ‘yan sanda a jihar Kano, wani shiri ne a karkashin shirin ‘yan sandan al’umma na gwamnatin jihar.
A cewar sa, wannan shiri ya biyo bayan yanayin tsaro da jihar Kano ta ke da shi, inda ya jaddada cewa wannan ba wani mummunan tunani ba ne.
Sanarwar ta kara da cewa, “An mayar da su ofishin ‘yan sanda, ba ‘yan sanda ba. Kalmomin 2 ba iri ɗaya ba ne. Wannan shiri da aikin gwamnatin jihar Kano ne a karkashin tsarin ‘yan sandan al’umma.
“A ganina, ba mummunan tunani ba ne gwamnati ta mayar da su jami’an tsaro masu amfani.
“Idan kun san Kano sosai, za ku fahimci ra’ayin gwamnati game da hakan. Don haka a yi nazarin Jihar Kano, a sanar da kai”.


