Mayaƙan kamfanin sojojin hayar Rasha na Wagner, Yevgeny Prigozhin, na ci gaba da nuna alhininsu kan hatsarin jirgin da shugaban kamfanin ke ciki.
A farkon makon nan ne Yevgeny Prigozhin ya bayyana cikin wani bidiyo da ke nuna ƙungiyar na ɗaukar sabbin mayaƙa a Afirka, watanni biyu bayan boren sojin da bai yi nasara ba da ya jagoranta.Image caption: A farkon makon nan ne Yevgeny Prigozhin ya bayyana cikin wani bidiyo da ke nuna ƙungiyar na ɗaukar sabbin mayaƙa a Afirka, watanni biyu bayan boren sojin da bai yi nasara ba da ya jagoranta.
An yi ta kunna kendura a kusa da furanni da hotunan shugaban Wagner da aka jera a wajen harabar ofisoshin kamfanin a biranen St Petersburg da Novosibirsk.
An yi ta kunna kendura a kusa da furanni da hotunan shugaban Wagner da aka jera a wajen harabar ofisoshin kamfanin a biranen St Petersburg da Novosibirsk.
Tun da farko wani shafin Telegram mai alaƙa da Wagner ya ce harbo jirgin aka yi, wanda ya faɗi da maraicen ranar Laraba.