fidelitybank

Mayakan ISWAP ta sake kai sabon hari a yankin Borno

Date:

Mayakan kungiyar ISWAP, wadda ake kira da Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, ta kai farmaki a garin Auno, a wani kauye dake karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

Rahotanni ya nuna cewa, maharan sun afkawa al’ummar garin da safiyar ranar litinin, wanda suka rika harba manyan bindigogi.

Lamarin da ya tilastawa mutane bazama, domin tsira da rayukansu tare da kasancewa a cikin gida, yayin da ake ci gaba da harbe-harbe kamar yadda wani soja ya shaida hakan.

Ya kara da cewa,”Sojojin sun yi galaba a kan ‘yan ta’addan ne a wani artabu da suka yi da su, wanda hakan ya sa suka tsere. Ba yanzu ba a iya tantancewa ba ko akwai wadanda suka jikkata. Ba zan iya cewa watakila an sace wani ba, harin ne da aka kai kan matafiya da ke bin babbar hanya a cikin al’umma,” inji majiyar.

Tun bayan rasuwar shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, kungiyar ISWAP ke kara karfafa gwuiwa a yankunan da ke kusa da tafkin Chadi.

Kwanan nan, ta nada Wali Sani Shuwaram, mai shekaru 45 a matsayin sabon Shugaban (Wali) na ISWAP a tafkin Chadi.

Mambobin kungiyar sun janye sauran daruruwan mayakan kungiyar Boko Haram na karkashin Shekau.

Rundunar sojin Najeriya ta sha yin ikirarin cewa an yi galaba a kan ‘yan ta’addan kuma a lokuta da yawa suna yin watsi da duk wani asarar da aka yi.

Kungiyar ta’addanci ta yi sanadin mutuwar sama da mutane 50,000 tare da raba miliyoyin mutane daga muhallansu, musamman a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe.

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp