Rahotanni daga jihar Borno ya tabbatar da cewa, mayaƙan ISWAP sun kashe aƙalla mutane 13 a ƙauyuka da dama a jihar.
An kai hare-haren ne a ƙauyuka huɗu, cikin kwanaki biyu.
Wasu mazauna ƙauyukan sun shaida wa manema labarai cewa, mayaƙan sun kuma sace mutane da dama.