Mayakan Boko Haram na ci gaba da mika wuya ga sojojin Najeriya, wanda a yanzu haka sun kai 470.
Rahotanni na nuni da cewa, daga cikin mayakan ta’addancin akwai manyan kwamandoji hamsin da iyalansu da suka mika wuya ga rundunar Operation Hadin Kai a kudancin jihar Borno.
Wannan na zuwa ne bayan luguden wauta da sojin saman Najeriya suka yi wa maboyar ‘yan ta’addan a yankin tafkin Chadi, inda suka halaka mayakan ta’addan masu tarin yawa.
Daily Trust ta rawaito cewa, ‘yan ta’addan sun fito daga dajin Sambisa a ababen hawa kusan goma inda kai tsaye suka tunkari sansanin sojoji da ke Gwoza, shelkwatar karamar hukumar Gwoza ta jihar.
Aliyu Muhammad wani mazaunin Gwoza ne ya ce, daruruwan ‘yan ta’addan a Gwoza ranar Talata. Sun bayyana a jigace kuma da yawa daga cikin ‘ya’yansu sun bayyana a yunwace. Idan za a tuna, shugaban Boko Haram, Sheikh Abubakar Ibn Al-Shekau ya bayyana Gwoza a matsayin Shedkwatar mulki ta Boko Haram a 2014, kafin dakarun sojin Najeriya su kwace garin a 2015.