‘Yan Boko Haram da na ƙungiyar Iswap 47 ne suka muƙa wuya ga sojojin haɗin gwiwa da ke yaƙi da Boko Haram a ƙasashen yankin Tafkin Chadi.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce mutanen da suka haɗa da maza bakwai da mata 9 da ƙananan yara 31, sun miƙa kansu ne a garin Kwatan Turare da ke Doron Baga a ƙaramar hukumar Kukawa na jihar Borno.
Sojojin sun ce binciken farko ya nuna cewa, mutanen sun tsere ne daga wani gari da ake kira Sharama da ke tsakiyar tsibirin Tafkin Chadi.
Daga cikin mutanen da suka miƙa wuya akwai, Mallam Muazu Adamu wani fitaccen mayaƙin ƙungiyar Boko Haram ɓangaren Shekau, da ya yi aiki ƙarƙashin kwamanda Alai Gana.
Mutanen sun shaida wa sojojin cewa suna gudanar da sana’ar noma a garin da suke kafin su yanke shawarar miƙa kansu.
Mallam Muazu Adamu ya miƙa kansa ga sojojin tare da iyalansa
Sojojin sun ce suna zurfafa bincike kan mutanen domin samun wasu ƙarin bayanai daga gare su.