Rundunar dakarun ƙasashen da ke yaƙi da ƙungiyar Boko Haram ta MNJTF ta samu nasarar karɓar tubabbun mayaƙan ƙungiyar su 46 tare da hannunta su ga hukumomin Chadi.
Babban kwamandan rundunar shiyya ta biyu Manjo Janar Djouma Youssouf Mahamat Itno, ne ya jagoranci miƙa tubabbn mayaƙan ga ƙasar Chadi.
An miƙa tsoffin mayaƙan ne a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar a Bagasola na ƙasar Chadi.
Ministan ayyukan gwamnatin ƙasar da kyautata zamantakewa na ƙasar Abdoulaye Mbodou Mbami ya ƙarbi tsofinmayaƙa a madadin gamnatin ƙasar.
Wannan wani ɓangaren na yunƙurin rundunar MNJTF da hukumomin ƙasashen da ke fama da matsalar Boko Haram, na ganin cewa mayaƙan ƙungiyar sun ajiye makamai tare da komawa cikin al’umma domin ci gaba da rayuwa.
Kungiyar Boko Haram dai ta shafe shekaru masu yawa tana kai hare-hare a ƙasashen yankin tafkin Chadi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, tare da raba miliyoyi da muhallansu.


 

 
 