Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce, duk wani mayaƙi na Hamas sunansa “mataccen mutum,” bayan taron farko na sabuwar gwamnatin gaggawa ta kasar.
Netanyahu da ɗan adawa Benny Gantz – tsohon hafsan soji – sun haɗa gwamnatin haɗaka domin tunkarar yaƙi a ranar Laraba, inda suka ajiye adawarsu ta siyasa.
Gantz ya ce lokaci ne na yaƙi kuma sabuwar gwamnatin da aka kafa a shirye take ta “shafe Hamas daga doron kasa”.