Fitaccen mawakin Najeriya Burna Boy zai yi wasa a wasan karshe na gasar Zakarun Turai na wannan shekara wanda za a yi a birnin Santanbul na Turkiyya.
Mawakin wanda kuma ya samu kyautar Grammy mai salon wakar afrobeat zai cace da ɗimbin mutane da za su halarci wasan karshen, a cewar wata sanarwa da UEFA ta fitar.
“Mun yi tanadi na musamman don cacewa da masoya kwallon kafa,” in ji Burna Boy gabanin wasan da zai yi a filin wasa na Atatürk Olympic.