Mawakin afrobeat Seun Kuti, ya yi magana a karon farko, tun bayan da aka sako shi daga hannun ‘yan sanda.
Mawakin wanda aka tsare a sashin binciken manyan laifuka, bincike da leken asiri na SCIID, Yaba a Legas, bisa umarnin wata kotun Majistare ta Yaba bisa laifin cin zarafin wani dan sanda, an bayar da belin mawakin ne a ranar Talata.
Da yake kai wa Instastory nasa jim kadan bayan an sake shi, Kuti ya gode wa duk wadanda suka tsaya masa a lokacin da yake cikin mawuyacin hali.
Ya rubuta, “Ina so in yi godiya mai zurfi ga duk wanda ya nuna mini wannan ƙauna. Duk abokaina da suka bayyana! Godiya ta musamman ga kyakkyawar matata @chefyeidekuti”.