fidelitybank

Mawakin da ya rasa Dala Biliyan 2 cikin sa’a 24 ya magantu

Date:

Wani Ba’amurke mawaki kuma mai zanen kaya, Kanye Omari West, wanda aka fi sani da Kanye West ko Ye, ya yi asarar dala biliyan 2 a cikin sa’o’i 24 bayan wasu kamfanoni da dama sun yanke alaka da shi saboda kalaman kyamar Yahudawa.

Wannan na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan wata mujallar kasuwanci ta Amurka, Forbes, ta sanar da cewa Kanye ba shi da wani matsayi a cikin jerin masu kudi a yanzu bayan da yarjejeniyarsa mai tsoka da Adidas ta kare.

Kamfanonin da suka yanke alaƙa da Kanye ya zuwa yanzu sun haɗa da Balenciaga, MRC (dakin nishaɗin da aka riga aka gama Ye Documentary), hukumar baiwar sa CAA, Adidas, Jaylen Brown da Aaron Donald, Foot Locker, The RealReal, T.J. Maxx, Madame Tussauds.

Da yake mayar da martani kan asarar, mawakin, a wani sako da ya wallafa a shafin Instagram, ya bayyana cewa mutanen shi ne ba kudin ba.

Ya rubuta, “Na yi asarar dala biliyan 2 a rana ɗaya, kuma har yanzu ina raye. Wannan maganar soyayya ce, har yanzu ina son ku; kudin ba ni ba ne, jama’a su ne ni.”

Har ila yau, makarantarsa, Donda Academy, ta shafa yayin da aka fitar da su daga gasar makarantar sakandare saboda maganganun Kanye.

latest news in nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...
X whatsapp