Shahararriyar mawaƙiyar nan Tina Turner wadda ta yi suna a duniyar waƙa ta mutu tana da shekara 83.
Mawaƙiyar, wadda aka haifa a Tennessee da ke Amurka, ta rera waƙoƙi da dama ciki har da River Deep, Mountain High da What’s Love Got to Do With It.
Waƙoƙinta na da nasaba da labarin rashin jin daɗin zamantakewarta da mijinta na farko, Ike Turner sannan ta ci gaba da samun nasara a fagen waƙa a shekarun 1980.
Turner dai ta shafe fiye da shekara 60 a duniyar mawaƙa sannan ta lashe kyaututtukan Grammys sau 12.
Tuni dai mawaƙa daga faɗin duniya suke ci gaba da alhinin mutuwarta inda suka bayyana marigayiyar a matsayin wadda suka tasirantu da waƙoƙinta.