Ministar fasaha da harkokin ƙirƙire-ƙirƙire, Hannatu Musa Musawa, ta buƙaci marubutan waƙoƙi da mawaƙa daga ko’ina cikin Najeriya su samar da wata waƙa ta musamman ga ƙasa.
Ta ce tana ganin yana da mahimmanci a sami waƙar da ke wakiltar ƙasar gaba ɗaya.
Ministar ta kara da cewa waƙar, wadda za ta zama sabon kirarin ƙasar, za ta taimaka wa mutane su ƙara yin imani da Najeriya da manufofinta
A cewar wata sanarwa da ofishin yada labarai na ministar ya fitar a ranar Talata, ta bayyana hakan ne jim kadan bayan naɗa ta a kan muƙamin.
“A gaskiya ina son mu samu wani sabon take na musamman da ke wakiltar Najeriya, ina fata marubuta waka da masu kade-kade daga sassa daban-daban na kasar nan za su fara tunanin hakan.” in ji sanarwar
Hannatu Musawa ta kuma yi alkawarin yin aiki tukuru domin ganin martabar Najeriya ta inganta.
Ta ce bai kamata a san Najeriya da munanan abubuwa kamar talauci da zamba da ta’addanci ba.


