Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce, ya amince da sabon mafi karancin albashi na 70,000 ga ma’aikatan jihar, saboda matsalar tattalin arziki da gwamnatin tarayya ta yi na cire tallafin man fetur.
Obaseki ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga ma’aikata, yayin bikin ranar May Day ta ma’aikata a filin wasa na Samuel Ogbemudia da ke birnin Benin.
Ya ce, ya kara mafi karancin albashin a jihar Edo daga Naira 40,000 zuwa Naira 70,000 duk wata, wanda hakan ya kai sama da kashi 75 cikin 100.
Obaseki, ya kuma ce ya yi karin ne, sakamakon irin jin jikin da ma’aikatan ke yin a shan wahalar rayuwar da ake fuskanta a kullum a fadin kasar nan.