fidelitybank

Matsalar tsaro ne ya sanya mu ka ƙasa gama gyaran wutar Arewa – TCN

Date:

Kamfanin rarraba wutar lantarki na ƙasa TCN, ya bayyana cewa aikin gyara layin samar da lantarki na Apir-Ugaji ya ɗauki tsawon lokaci ba a kammala ba ne saboda matsalar tsaro a yankin.

Da yake magana a wani taron manema labarai a yau Talata, Manajan Darektan, kamfanin Injiniya Abdulaziz Sule, ya ce injiniyoyin da ke gyaran suna aiki ne bisa kulawar jami’an tsaro -sojoji, kuma da zarar ƙarfe 6 na yamma ya yi dole ne su bar wajen su je wajen da babu matsalar tsaro su kwana sannan da safe su koma bakin aiki.

Amma duk da haka ya ce, za a kammala aikin a cikin kwana biyu ko uku a hanyar wadda take da wani layin na samar da lantarki ga Kano da sauran manyan birane a arewacin Najeriya.

Shugaban ya kuma ce shi ma layin na biyu wanda aka lalata wajen turakuna biyar nasa zai dawo bakin aiki aƙalla zuwa ranar Lahadi – cikin kwana biyar kenan.

Injiniya Sule ya ƙara da cewa da zarar an kammala gyaran layukan biyu, za a iya aikawa da wutar lantarkin da aƙalla ta kai yawan megawatt 500 zuwa 600 ga yankin arewacin Najeriyar.

A kan abin da kamfanin yake yi kuma don hana ɓarnata kayan samar da wutar lantarkin, ya ce suna haɗa kai da al’ummomin yankunan, inda har ma suna ba su kuɗin sufuri da kuma waya don sheda msu duk wani abu da suka gani da zai yi illa ga layukan samar da wutar.

Sannan ya ce suna kuma haɗa kai da jami’an tsaro – sojoji da ‘yansanda da rundunar tsaro da kai ɗauki (Civil_Defense…), domin tabbatar da ganin suna sintiri a wuraren kayan samar da lantarkin

www.nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp