Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya roki ‘yan Nijeriya da kada su yanke imani da al’ummar kasar nan, domin kuwa tabbas za su shawo kan kalubalen da suke fuskanta.
A cikin sakonsa na ranar dimokuradiyya a ranar Lahadi, ya tabbatar musu da cewa, kamar yadda a karshe demokradiyya ta yi nasara a kan mulkin kama-karya, wadata za ta shawo kan talauci, zaman lafiya zai wuce tashin hankali, tausayi zai shawo kan kiyayya, kuma nagari zai kawar da mugunta.
Tinubu ya kuma yi fatan cewa bayan wani lokaci mai tsanani ga kasar nan, adalci, tsaro, da bunkasar tattalin arziki za su ziyarta da zama a kowace lungu, gida, kauye, da birni.
Ya kara da cewa, ruhin ranar 12 ga watan Yuni zai fadada ya zama ruhin Najeriya da daukaka da makomar al’umma.