Gwamnan jihar Zamfara, Hon Bello Mohammed Matawalle ya amince da sake yin garambawul gawasu mambobin majalisar zartarwa sa.
A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Kakiru Balarabe ya raba wa manema labarai a Gusau babban birnin jihar, ya ce Hon. Nasiru Zarumi Masama daga ma’aikatar matasa da ci gaban wasanni ya koma ma’aikatar ilimi.
Sanarwar ta bayyana cewa Hon. Zainab Lawal Gummi daga ma’aikatar ilimi ta koma ma’aikatar harkokin mata da yara;
Hon. Lawal Abubakar daga ma’aikatar zamantakewa da cigaban al’umma yanzu ya koma ma’aikatar matasa da wasanni, yayin da Hon. Muhammad Abubakar Gummi daga ofishin sakataren gwamnatin jiha (SSG) ya koma ma’aikatar zamantakewa da ci gaban al’umma.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, sun fara aiki nan take.


